Hatsari ba sai a Mota ba: Mutane 5 sun gamu da ajalinsu yayin da Kwalekwale ta kifa dasu

Hatsari ba sai a Mota ba: Mutane 5 sun gamu da ajalinsu yayin da Kwalekwale ta kifa dasu

Tsautsayi baya wuce ranarsa , kuma dama ai idan ajali ya yi kira, toh ko ba ciwo sai an tafi, akalla mutane biyar ne suka gamu da ajalinsu yayin da wani Kwalekwale ya kifa a cikin tafkin Legas, inji rahoton Legit.ng.

Wannan mummunan lamari ya faru ne da yammacin ranar Laraba, 25 ga watan Yuli a Tafkin Ikorodu na jihar, inda Kwalekwalen na zamani ya kifa yana tsaka da tafiya a tsakiyar teku, sai dai ana ta binciken adadin mutanen da suka bace.

KU KARANTA: Ruwa ba sa’an Kwando ba: Daliban Kaduna sun lallasa na kasar Amurka a gasar Duniya

Hatsari ba sai a Mota ba: Mutane 5 sun gamu da ajalinsu yayin da Kwalekwale ta kifa dasu

Hatsari

Manajan hukumar bada agajin gaggawa na jihar Legas, LASEMA, Adesina Tiamiyu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace tuni aka garzaya da gawarwakin mutanen da suka mutu zuwa dakin ajiyan gawa na Asibitin Ikorodu, sun kunshi Namiji daya da Mata biyar.

Adesina ya kara da cewa sun ceto mutane biyar da suka hada da Mata hudu da namiji guda daya, haka zalika yace suna cigaba da bincike a cikin ruwa sakamakon kwalekwalen na dauke da mutane ashirin ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel