Soja wuta Soja: Dakarun Sojan sama sun kama yan bindiga 16 a jihar Zamfara

Soja wuta Soja: Dakarun Sojan sama sun kama yan bindiga 16 a jihar Zamfara

Gungun dakarun rundunar Sojan sama na 207 dake jibge a garin Gusau na jihar Zamfara ta sanar da kama yan bindiga guda goma sha shidda a yayin da take aikin kakkabe yan bindiga daga jihar mai taken ‘Operation Sharan Daji.’

Legit.ng ta ruwaito shugaban Dakarun mai suna Group Captain Caleb Olayera ne ya bayyana haka a yayin daya karbi bakoncin babban hafsan Sojan sama, Saddique Abubakar a ziyarar gani da ido daya kai garin Gusau.

KU KARANTA: Ruwa ba sa’an Kwando ba: Daliban Kaduna sun lallasa na kasar Amurka a gasar Duniya

Soja wuta Soja: Dakarun Sojan sama sun kama yan bindiga 16 a jihar Zamfara
Saukar Saddique

A yayin ziyarar tasa, Abubakar ya sanar da turo karin manyan kayan aiki da suka hada jiragen yaki da motoci zuwa jihar Zamfara daga sassan kasar nan duk dan tabbatar da tsaron dukiya da rayukan al’ummomin dake jihar Zamfara.

Caleb yace suna gudanar da samame ta sama, da kuma yawon sintiri da na leken asiri a cikin jirgin sama, kuma a dalilin haka sun kama wani kasurgumin dilan miyagun kwayoyi, wanda tuni suka mika shi ga hukumar yaki da sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi, NDLEA.

Soja wuta Soja: Dakarun Sojan sama sun kama yan bindiga 16 a jihar Zamfara
Tare da Sojoji

Caleb ya cigaba da cewa sun kwato bindigu guda uku, da alburusai da dama daga hannun yan bindiga, sa’annan sun kama yan bindiga guda 16, Sojojin sun ceto mutane takwas da aka yi garkuwa dasu, biyar daga cikinsu Yansanda ne.

Dayake nasa jawabin, Abubakar ya jinjina ma jarumtar runduna ta 207, musamman ta yadda take kokarin kare rayukan mutanen jihar Zamfara duk da hatsarin da aikin yake tattare da su, daga nan ya shaida musu cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na sane da aikinsu, kuma ya yaba musu.

Soja wuta Soja: Dakarun Sojan sama sun kama yan bindiga 16 a jihar Zamfara
Tare da hafsoshi

Daga karshe Abubakar ya bayyana matakan da gwamnati ke dauka don inganta walwaalar Sojojin, sa’annan ya umarci manyan kwamandojin rundunar dasu tabbata sun share ma Sojojin hawayensu, musamman game da kalubalen da suke fuskanta,kamar yadda Caleb ya zayyanosu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng