Wata duniya zata sakko kusa da tamu ranar 31 ga wannan watan - NASA
- Tazarar dake tsakanin duniyoyin bazata wuce Kilomita Miliyan 57.6 ba.
- Hakan bazai kuma faruwa ba sai a shekara 2287.
Duniyar Mars zata sakko kusa da tamu duniyar bayan shekaru 15 da aka kwashe hakan bai faru ba, hakan zai faru ne a ranar 31 ga watan Yuli, duniyar zata canja yanayi zuwa ja da kuma girma wanda zaiyi sauki wajen gano hakan, cewar hukumar ta NASA dake kasar Amurka.
Tazarar dake tsakanin duniyoyin biyu bazata wuce Kilomita Miliyan 57.6 a ranar 31 ga watan Yulin nan.
Hasken Duniyar ta Mars zai fara tunkarowa tun daga ranar 27 zuwa 30 ga watan Yuli.
DUBA WANNAN: Rashin aikin yi, da tsadar rayuwa sune babbar matsalar Najeriya
"Hasken bazaikai na duniyar Venus ba amma saboda jan da take dashi, hakan zai bayyana a sararin samaniya". Cewar Harry Augensen daya daga cikin masu bincike a jami'ar Widener.
Kafin duniyar Mars ta tunkaro mu a ranar Juma'a za'a samu sabani wanda hakan na nufin bayyanar rana da kuma Mars a tare suna kallon juna kamar yanda zamu gani a kasa.
A ranar kuma za'a samu husufin wata a yankunan Africa, Asia, Australia, Europe da kuma South America.
Mars da duniyar mu sunyi kusa da juna matuka shekarar 2003 inda a wancan lokacin akwai tazarar Kilomita Miliyan 55.7 wanda shine mafi kusa.
Irin hakan ya faru shekaru 60,000 kuma bazai kara faruwa ba sai a shekarar 2287, cewar NASA.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng