Hotuna daga ganawar Buhari da Sanatocin APC a daren jiya
A daren jiya ne shafin yada labarai na Legit.ng ya kawo maku rahoton cewar shugaba Buhari zai gana da mambobin majalisar dattijai na jam'iyyar APC a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaba Buhari da 'yan majalisar dattawan sun gana ne a dakin taro na uwargidan shugaban kasa wato First Lady Conference room da misalin karfe 9.00 na daren jiya, Laraba.
Legit.ng ta fahimci cewa, babu tabbataccen dalilin wannan ganawa da za aka gudanar da ita cikin gaggawa a farfajiyar ta fadar shugaban kasa, duk da wasu na ganin ba zata rasa nasaba da batun ficewa daga jam'iyyar APC da wasu sanatoci 15 suka yi ba ranar Talata.
DUBA WANNAN: An kulla sharudan aiki tare tsakanin Kwankwaso da Shekarau a PDP ta Kano
A ranar Talatar da ta gabata ne Sanatoci 15 suka yi kaura daga jam'iyyar ta APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP da kuma sabuwar jam'iyyar ADC (African Democratic Congress) ta tsohon shugaban kasa Obasanjo.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng