Shugaba Buhari zai gana da Sanatocin APC a daren yau Laraba
Kamar yadda shafin jaridar nan ta The Nation ta ruwaito, mun samu rahoton cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gana da Sanatocin jam'iyyar sa ta APC a fadar sa ta Villa dake babban birnin kasar nan na Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaba Buhari da dattawan za su gana ne a dakin taro na First Lady Conference room da misalin karfe 9.00 na daren yau Laraba.
KARANTA KUMA: Mun yiwa 'yan Najeriya 31m shaidar 'Yan 'Kasa - NIMC
Legit.ng ta fahimci cewa, babu tabbataccen dalilin wannan ganawa da za a gudanar da ita cikin gaggawa a farfajiyar ta fadar shugaban kasa.
A ranar Talatar da ta gabata ne Sanatoci 14 suka yi kaura daga jam'iyyar ta APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP da kuma jam'iyyar ADC (African Democratic Congress).
A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, mataimakin kakakin jam'iyyar ta APC, Yekini Nabena, yayi kira kan fatattakar shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki daga jam'iyyar sakamakon adawa da jam'iyyar sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng