2019: Shagari ya kaddamar da takarar gwamna a jihar Sakkwato
A yau Laraba, tsohon ministan albarkatun ruwa, Alhaji Mukhtar Shagari, ya kaddamar da takarar gwamna a jiharsa ta Sakkwato karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019 mai zuwa.
Shagari wanda ya yi aike a matsayin mataimakin gwamna karkashin tsohon gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko ya tabbatar wa al'umma cewa kwarewarsa da gogewa wajen sanin bukatun al'umma ne yasa yake son fitowa takarar.
Duk da yace babu wani 'dan takara da zai iya taka masa birki a zaben shekarar na 2019, Shagari yace siyasa sadaukawarce wajen ganin cewa an biya wa al'umma bukatunsu ba wai mutum ya gina kansa ba.
DUBA WANNAN: Tsalle-Tsallen 'yan siyasa: Wani dan majalisar PDP ya fice daga jam'iyyar
Tsohon mataimakin gwamnan yace muddin ya yi nasarar zama gwamnan jihar, cikin abubuwan da zai fara kaddamarwa shine duba marasa lafiya kyauta, samar da ayyuka da ilimi ga al'ummar jihar.
A yayin da yake jawabi ga taron masoyansa a sakatariyar PDP dake jihar, Shagari yace nan da kankanin lokaci za'a samu cigaba ta bangaren gine-gine da gina al'umma a jihar irin wanda ba'a taba samu ba a tarihin jihar.
Kazalika, Shagabari yace dadewar da ya yi a siyasa, da kwarewa wajen mulki da kuma iya harka da al'umma da kirkirar hanyoyin sawwaka rayuwar al'umma na cikin abubuwan da zasu taimaka masa wajen samun nasara a zaben na 2015.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng