Yanzu-Yanzu: Matasan Benuwe sun hana Ortom fita daga gidansa, sun bukaci ya fice daga APC

Yanzu-Yanzu: Matasan Benuwe sun hana Ortom fita daga gidansa, sun bukaci ya fice daga APC

A yau laraba ne matasan jihar Benue suka fito kwansu da kwarkwata suka tare kofar gidan gwamnatin jihar saboda basu amince gwamna Samuel Ortom ya tafi Abuja don halartar taron sulhu da aka shirya ba.

A dai shirya cewa gwamna Ortom zai gana da shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole tare da wasu jiga-jiga jam'iyyar don kokarin ganin gwamnan bai fice daga jam'iyyar ba.

Matasan sun bukaci gwamnan ya fice daga jam'iyyar ta APC kamar yadda Channels tv ta wallafa.

Shugaban matasan da ke zanga-zangar, Dave Ogbole, ya kallubalanci gwamnan ya markade su da motocinsa muddin yana son dole sai ya hallarci taron.

Yanzu-Yanzu: Matasan Benuwe sun hana Ortom fita daga gidansa, sun bukaci ya fice daga APC

Yanzu-Yanzu: Matasan Benuwe sun hana Ortom fita daga gidansa, sun bukaci ya fice daga APC

DUBA WANNAN: Tsalle-Tsallen 'yan siyasa: Wani dan majalisar PDP ya fice daga jam'iyyar

Mr Ogole yace, "Idan har gwamna Ortom ya dage cewa sai ya hallarci taron sulhun a Abuja, tabbas sai rasa goyon bayan al'ummar jiharsa."

Duk da irin rokon da gwamnan ya yi da matasan su bashi hanya domin ya tafi Abuja ya hallarci taron saboda warware matsalolin dake faruwa a jam'iyyar ta APC, matasan sun doge kan bakarsu har sai da gwamnan da tawagarsa suka koma gida.

Duk da haka matasan sun cigaba da gudanar da zanga-zangarsu a kofar gidan gwamnatin domin tabbatar da cewa gwamnan bai sulale ya tafi taron ba bayan sun watse.

Idan mai karatu bai manta ba, Legit.ng ta kawo muku rahoto inda gwamna Ortom ya shaida wa wata tawagar kwararu na jihar Benue cewa babu abinda zai sa ya cigaba da zama a jam'iyyar ta APC.

Ya furta hakan ne bayan taron sulhu na farko da ya yi da shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole a sakatariyar jam'iyyar dake Abuja.

Gwamna Ortom ya sha fadin cewa al'ummar jihar Benue ne zasu yi masa zabin jam'iyyar da zai koma saboda dama da bazarsu yake rawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel