Matata bata nan shi yasa na zakke ma Diyata – Inji wani jarababben Uba

Matata bata nan shi yasa na zakke ma Diyata – Inji wani jarababben Uba

Wani jarababben mutumi dan asalin garin Daura na jihar Katsina, Basiru Audu ya shiga hannun jami’an Yansandan jihar Neja sakamakon kama shi da suka yi bayan ya zakke ma diyarsa mai shekaru shidda, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar 16 ga watan Yuli, a gidansu dake titin Landan, cikin garin Minnan jihar Neja, inda Audu ya lallaba dakin diyarsa, ya kwanta da ita.

KU KARANTA: Abin nema ya samu: Fayoshe ya kai ma Saraki ziyarar ‘Ana tare’

Makwanbtan wannan mutumi ne suka fallasa mummunan aika aikan da yake aikatawa, bayan sun lura yarinyar tana wani irin tafiya, da suka tambayeta sai tace mahaifinta ne ya saka mata wani abu a farjinta.

Matata bata nan shi yasa na zakke ma Diyata – Inji wani jarababben Uba

Basiru Audu

Sai dai majiyar ta kara da cewa wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da mahaifiyar yarinyar ta yi tafiya, inda ta kai ziyara garinsu, Dauran jihar Katsina, wannan yasa ya danganta rashin matartasa a gida ga wannan aika aika da ya tafka.

“Laifin Matata nake gani saboda bata gida, domin rashin zamanta ne ya jefa ni cikin wannan abin kunya, har ta kai ga na zakke ma diyata, na zaku kwarai da gaske a daren nan don na kwanta da mace, amma tunda dai Matata bata nan dole kawai na san na yi, wannan ne ya sanya ni zakke mata.” Inji shi.

Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Muhammad Abubakar ya bayyana cewa wanda ake zargin bai baiwa sharia wahala ba, kuma ya yi danasanin abinda ya aikata, inda ya kara da cewa; “Idan har Uba zai kwanta da Diyarsa, ina ganin alama ne na karshen Duniya.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel