Gwamna Masari ya nada sabon shugaban Ma'aikata na jihar Katsina

Gwamna Masari ya nada sabon shugaban Ma'aikata na jihar Katsina

Mun samu rahoton cewa gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya rantsar da sabon shugaban ma'aikata na jihar sa, Alhaji Idris Tune.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, Tune ya maye gurbin Alhaji Garba Sanda, wanda ya ajiye aiki sakamakon shekarun sa da suka kai munzali na ritaya daga aikin gwamnati a kwana-kwanan nan.

A yayin bikin rantsar da sabon shugaban na ma'aikata, Masari ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta ci gaba bayar da muhimmanci wajen inganta harkokin ma'aikata sakamakon kasancewar su masu rike da akalar kowace gwamnati.

Gwamna Masari ya nada sabon shugaban Ma'aikata na jihar Katsina
Gwamna Masari ya nada sabon shugaban Ma'aikata na jihar Katsina
Asali: Depositphotos

Masari ya jaddada muhimmancin hadin kai tare da cudanya tsakanin kanana da manyan ma'aikata domin tabbatar da ingancin hidimar gwamnati a jihar.

KARANTA KUMA: Jarumta: R- APC ta yabawa 'yan Majalisa da suka sauya sheka

Ya shawarci sabon shugaban na ma'aikata akan daukan darussa na kwarewar aiki irin ta wanda ya ci gajiyar kujerar sa domin cimma manufa ta kujerar sa tare da sauke nauyin da ya rataya a wuyan sa cikin gaskiya da kuma adalci.

Kamar yadda rahotannin suka bayyana, an haifi Tune a shekarar 1963 cikin karamar hukumar Ingawa ta jihar. Ya kuma fara aikin gwamnati a shekarar 1988 inda ya kai mukamin sakatare na din-din-din a shekarar 2008.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng