Yanzu - yanzu: Buhari sunyi ganawar sirri da Babban Sufeton 'Yan Sanda

Yanzu - yanzu: Buhari sunyi ganawar sirri da Babban Sufeton 'Yan Sanda

A yau dinnan ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari, suka yi wata ganawar sirri tsakanin sa da Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya, (IGP) Ibrahim Idris, a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja

Yanzu - yanzu: Buhari sunyi ganawar sirri da Babban Sufeton 'Yan Sanda
Yanzu - yanzu: Buhari sunyi ganawar sirri da Babban Sufeton 'Yan Sanda

A yau dinnan ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari, suka yi wata ganawar sirri tsakanin sa da Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya, (IGP) Ibrahim Idris, a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja.

Har ya zuwa yanzu dai ba bayyana ainahin mai suka tattauna akai ba.

DUBA WANNAN: 2019: Har yanzu mu muke da mafi rinjaye - Jam'iyyar APC

Ganawar ta su ta faru ne jim kadan bayan labari ya fita cewar jami'an tsaro sun yiwa gidan shugaban majalisar dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki tsinke, da mataimakin sa Sanata Ike Ekweremadu.

A jiya ne dai hukumar 'yan sandan kasar nan ta bukaci Saraki da ya bayyana a gabanta domin amsa wasu tambayoyi wadanda suke da alaka fashin da aka yi a garin Offa dake jihar Kwara.

Hukumar 'yan sandan ta bukaci Saraki da ya bayyana a gabanta yau da misalin karfe 8 na safe, amma bai bayyana har lokacin da shugaban hukumar 'yan sandan suka gana da shugaba Buhari.

Rashin bayyanar shi ya saka hukumar 'yan sandan sanar da cewar zata yi amfani da karfin ta domin kamo shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng