Ko a jikin mu canja shekar da kuke yi - Jam'iyyar APC
Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole ya ce Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da kuma sauran duk wadanda suka canja sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) basu da wani muhimmanci a cikin jam'iyyar APC
Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole ya ce Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da kuma sauran duk wadanda suka canja sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) basu da wani muhimmanci a cikin jam'iyyar APC.
DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram sun kashe mutane 18, sun kuma sace mata 9 a yankin Chadi
Ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan ganawar shi da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce jam'iyyar APC ko kadan bata damu da komawar Sanatoci da 'Yan majalisar wakilai suka yi ba zuwa jam'iyyar PDP.
Majiyar mu Legit.ng ta kawo muku rahoton canja shekar sama da mahukunta 50 na gwamnatin tarayya daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP.
Oshiomhole yace a zaben shekarar 2015 shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu kuri'u fiye da dukkanin wadanda suka juya wa jam'iyyar baya a mazabunsu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng