Ba da kudi ka shiga wasa: An gano barnar da ake yi a wasan kwallon kasar nan
- Kocin Najeriya Salisu Yusuf yana karbar cin hanci domin a sa wasu ‘Yan wasa
- Ana zargin a kan ba Kocin har N360, 000 ya zabi ‘Yan wasan da za su buga wasa
- A kan kuma yi masa alkawari da makudan kudi inda har abubuwan sun yi kyau
Mun samu labari cewa ana tafka cuwa-cuwa a harkar kwallon kafan Najeriya inda ake ba Kocin da ke kula da ‘Yan wasan watau Salisu Yusuf kudi domin a saka wasu cikin wasa.
Ana biyan Salisu Yusuf N360, 000 domin ya saka ‘Dan wasa cikin wadanda za su buga Gasar 2018 CHAN. Ana shiryawa ne da Kocin cewa za a ba shi kudi idan ‘Yan wasan sun samu fita zuwa Turai idan Tauraruwar su ta haska.
KU KARANTA: 'Dan wasa Ahmed Musa ya shirya kai mutane kara a Kotu
Wasu ne su kayi bincike su ka gano yadda ake karbar cin hanci da rashawa a harkar kwallon inda asirin ya tonu bayan da aka ga Kocin Kasar yana karbar kudi daga wasu da su ka nuna masa cewa Wakilan ‘Yan kwallon sa ne.
Kocin Kasar ya karbi kudi domin ya tafi da wasu ‘Yan kwallo zuwa Gasar cin kofin Nahiyar Afrika da aka yi bana a Kasar Morocco. Najeriya ta samu zuwa wasan karshe a Gasar amma ta sha kashi da ci 1-4 a hannun masu garin.
Sai an ba Kocin na Najeriya kudi ne dai ya ke sa wasu ‘Yan kwallon tare da yarjejeniyar cewa idan ‘Yan wasan su ka samu zuwa Turai za a ba shi kashi 15% na cinikin da aka yi a nan gaba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng