Kabilun Taraba 5 sun shiga yarjejeniar zaman lafia da Fulani

Kabilun Taraba 5 sun shiga yarjejeniar zaman lafia da Fulani

Kabilar Nyandan da wasu hudu a karamar hukumar Lau dake jihar Taraba, a ransar Asabar sun shiga yarjejeniyar zaman lafiya da Fulani.

An shiga yarjejeniyar zaman lafiyan ne a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki na dukkanin kabilun a Mayolope wani gari dake iyaka tsakanin jihohin Adamawa da Taraba.

An yarda cewa dukkanin kungiyoyin su janye maakansu; yayinda aka umurci jami’an tsaro das u kama duk kungiya ko mutumin da suka gani da makamai.

Kabilun Taraba 5 sun shiga yarjejeniar zaman lafia da Fulani
Kabilun Taraba 5 sun shiga yarjejeniar zaman lafia da Fulani

An kuma amince da cewa kungiyoyi da Fulani su kakkabe dukkanin fitina a yankunan sannan a kama duk wani mai laifi da aka kama a wajen.

KU KARANTA KUMA: 2019: PDP ta kira taron masu ruwa da tsaki na gaggawa kan bukatar R-APC

Kungiyoyin sun daura laifin akansu da suka bari wasu daga waje suka shiga tsakaninsu har suka ci galaba wajen hada su fada.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng