Wani matashi ya zartar da hukuncin Zina akan wasu abokansa guda 2

Wani matashi ya zartar da hukuncin Zina akan wasu abokansa guda 2

Rundunar Yansandan jihar Borno ta sanar da kama wani matashi mai shekaru 20, Hassan Garba da laifin kashe wasu mutane biyu Hussaini Alhassan da Naziru Haruna akan laifin zina a karamar hukumar Biu na jihar Borno.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan Yansandan jihar, Damian Chukwu ne ya sanar da haka a inda yace Hassan Garba ya kashe Hussaini mai shekaru 20 da Naziru mai shekaru 19 ne saboda yana zarginsu da aikata zina, don haka ya zama wajibi a gareshi ya yanke musu hukuncin kisan da ya hau kansu

KU KARANTA: Wani matashin Tela mai shekaru 19 ya aikata ma yar uwarsa danyen aiki a Borno

“A ranar 18 ga watan Mayu ne Hussai dauke da adda ya kai ma Alhassan da Haruna hari yayin da suke cikin barci, wanda hakan yayi sanadin mutuwarsu, inda yace yayi hakan ne domin yanke musu hukuncin da ya dace dasu, sakamakon mazinata ne su.” Inji kwamishina.

A wani labarin kuma Yansandan jihar sun samu nasarar kama wani lebura mai shekaru 19, Inusa Abubakar, wanda ya kashe Maigidansa Ba’ana Bukar mai shekaru 24 a ranar 26 ga watan Mayu.

Kwamihina Damian ne ya sanar da haka, inda yace Inusa ya yi amfani da wuka ne wajen kashe Maigidan nasa a daidai lokacin da suke aiki a wani kango dake unguwar Pompomari dake garin Maiduguri, sa’annan ya garzaya zuwa gidan mamacin, inda ya kashe kudi naira dubu sittin da biyu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel