Hajjin Bana: Yau za a fara jigilar maniyyatan Najeriya, duba hotuna
A yau, Asabar, ne za a fara jigilar maniyyata aikin Hajjin bana daga Najeriya zuwa kasar Saudiyya.
Hukumar jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON) ce ta sanar da hakan da yammacin jiya, Juma'a tare da bayyana cewar ta kammala shiri tsaf domin fara aikin jigilar maniyyatan.
Tuni kasar Saudiyya ta fara gudanar da shirye-shiryen fara karbar bakin alhazai da zasu yi aikin Hajjin bana.
DUBA WANNAN: Ku rage yawan haihuwa domin 'ya'yanku su samu ilimi - Ganduje
Kakakin hukumar NAHCON, Fatima Usara, ta bayyana cewar za a fara jigilar ne a yau Asabar da alhazan jihar Kogi a filin jiragen sama na kasa da kasa dake Abuja da misalin karfe 11:00 na safe.
Kazalika ta sanar da cewar za a fara jigilar maniyyatan na jihar Kogi ne a jirgin saman kamfanin MAX Air da zai dauke su kai tsaye zuwa Madina.
Fatima ta shawarci alhazan da su kasance masu hakuri da irin jerin tantancewa da kasar Saudiyya ke yiwa baki da zasu shiga kasar tare da bukatar su zama wakilan Najeriya nagari yayin gudanar da ibadar aikin Hajji.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng