Tirkashi: DPO da wasu 'yan sanda sun lallasa Alkali da lauyoyi a kotu, duba dalili
Rikici ta barke a kotun majisatre dake Ngor a karamar hukumar Ngor ta jihar Imo a ranar Talata bayan wasu 'yan sanda sun kutsa cikin kotun inda suka yiwa alkaliyar kotun, Ngozi Onyenemezu duka saboda wai ta saki wasu da ake zargi da fashi da makami.
Lauyoyin dake kare wadanda ake tuhuma, Emma Eke da Chukwuemeka Anyanwu suka wai sun sha duka kuma daga baya aka tisa keyarsu zuwa ofishin 'yan sanda masu binciken manyan laifuka SCIID dake owerri.
Mataimakin sakataren Kungiyar Lauyoyin Najeriya reshen jihar Owerri, Chinedu Agu, ya shaidawa manema labarai a ranar Juma'a cewa 'yan sandan sun yiwa Alkaliyar da kuma lauyoyin duka a kotun.
Ya bayyana lamarin a matsayin rashin biyaya ga doka kuma ya zama dole a dauki matakin gyara a kai.
DUBA WANNAN: Har yanzu ina kan baka ta na ficewa daga jam'iyyar APC - Gwamna Ortom
Yace an gurfanar da mutane uku a kotun Majistare ta Umuneke Ngor a ranar Litinin inda lauyoyin dake kare wanda ake tuhumar, Eke da Anyanwu suka bukaci kotun tayi watsi da tuhumar saboda a cewarsu ba'a bi ka'ida ba wajen shigar da karar kuma zuka nemi a saki wadanda aka gurfanar.
Bayan kotu ta saurari hujojin lauyoyi daga bangarorin biyu, ta zartar da hukuncin watsi da tuhumar. Watsi da karar ya sanya 'yan sanda suka tayar da hayaniya a kotun.
"'Yan sandan sun yiwa alkalin barazana kuma suka sake kama wadanda ake tuhumar, kotun tayi kokarin hana hakan daga nan ne 'yan sandan suka tasarwa alkalin inda ya arce zuwa ofishinsa ya buya.
"'Yan sandan karkashin jagorancin DPO sun tafi ofishin Alkalin suka bukaci ya bude kofar ko kuma su balle kofar, sun kuma zargi shi da karaban cin hanci. Bude kofar ke da wuya sai DPO da sauran 'yan sandan suka far masa da duka.
"Sai daga baya Area Kwamanda ne yazo ya ceci Alkalin daga hannun 'yan sandan," inji shi.
Sai dai kakakin 'yan sanda na jihar, Andrew Enwerem, ya musanta cewa 'yan sandan sun doki Alkalin. Yace lauyoyi biyu dake kare wadanda ake zargi da aikata fashi da makami ne suka kaiwa 'yan sandan hari yayin da suke gudanar da aikinsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng