'Yan sandan Najeriya sun cafke gawurtaccen barawon mota da motocin sata na alfarma 2 a Katsina
Jami'an 'yan sandan Najeriya dake a jihar shugaban kasa ta Katsina a can yankin Arewa maso yammacin Najeriya sun sanar da samun nasarar damke wani gawurtaccen marawon motoci da motocin sata har biyu.
Wanda aka kama da motocin da ake kyautata zaton na sata ne, mai suna Wadatau Lawan dan asalin jihar Sokoto ne kamar dai yadda jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, SP Gambo Isa ya sanar da manema labarai a jihar.
KU KARANTA: Buhari ya sha alwashin maido da martabar Arewa
Legit.ng ta samu cewa da yake karin bayani, SP Gambo ya bayyana cewa jam'ian nasu na 'yan sanda sun cafke barawon ne a garin Malumfashi na jihar kuma yanzu haka suna kan binciken lamarin.
A wani labarin kuma, Akalla mutane 30 ne suka rasa rayukan su yayin da kuma da yawa suka bace bat har yanzu ba'a gansu biyo bayan wani mummunan harin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai wa wasu matafiya akan hanyar Dikwa zuwa Ngala a jihar Borno.
Wani ganau ya shaidawa majiyar ta Daily trust a wayar tarho cewa akalla motoci 27 ne dauke da mutane da kayayyakin masarufi 'yan ta'addan suka tare suna harbi kafin daga bisani mutanen ciki su tsere.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng