Yan bindiga sun kashe mutane 2 sannan sun raunata wasu a harin kasuwar Zamfara – Yan sanda
Rundunar yan sandan Zamfara a ramar Juma’a ta tabbatar da kisan mutane biyu bayan wani hari da wasu yan bindiga suka kai kasuwa a kauyen Karakai a karamar hukumar Bungudu dake jihar.
Kakakin yan sandan jihar, SP. Muhammad Shehu ya bayyana hakan a wata sanarwa day a gabatar ga manema labarai a Gugau a ranar Juma’a.
“Wasu yan bindiga sunyi harbe-harbe a kasuwa, mun samu rikodin mutuwar mutane biyu yayinda wasu suka jikkata.
"A lokacin harin, tawagar yan sanda a kasuwar sun kasa musayar wuta da maharani domin gujema ci gaba da kashe mutane da asarar kayayyaki.
“Maharan sunyi amfani da cunkoson mutane dake kokarin gudu wajen tserewa.
KU KARANTA KUMA: Obasanjo na son sake shugabantar Najeriya ne ta kofar baya – Oshiomhole
“Lamura sun daidaita a wajen tare da tawagar yan sanda dake sunturi domin lura da wurin da abun ya afku.
“Ana gudanar da bincike domin kama maharan” cewar shi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng