Mutuwa riga: Janar IBB ya yi juyayin mutuwar wasu manyan yan Najeriya guda biyu

Mutuwa riga: Janar IBB ya yi juyayin mutuwar wasu manyan yan Najeriya guda biyu

Tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasa Babangida ya bayyana alhininsa da mutuwar wasu manyan mutane biyu yan Najeriya da suka rasu a wannan satin, tsohon babban sufetan Yansandan Najeriya, Ibrahim Coommassie da tsohon Alkalin Alkalai, Aloysius Katsina Alu.

KU KARANTA: Ambaliyar Katsina: Yadda ya ruwa ya yi awon gaba da wata jaririya yar watanni 3

IBB ya bayyana wannan alhini ne a cikin wata sanawar da ya fitar a ranar Juma’a, 20 ga watan Yuli a garin Minna na jihar Neja, inda yace ya kadu da samun labarin mutuwar mutanen biyu, sa’annna ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, da ma al’ummar Najeriya gaba daya.

Mutuwa riga: Janar IBB ya yi juyayin mutuwar wasu manyan yan Najeriya guda biyu

Katsina Alu da Coommassie

“Na sani a lokacin da Coommassie yake babban sufetan Yansanda mutum ne jajirtacce, kuma baya wasa wajen shawon kan duk wani lamari da ka iya kawo matsala ga zamanlafiya a Najeriya, haka zalika Katsina Alu alkali ne ba shi da tsoro.

“Dukkaninsu sun bauta ma kasar nan a lokacin da take cikin mawuyacin hali, tare da zaunar da kasar lafiya, don haka ba zamu taba mantawa dasu ba.” Inji shi.

Daga karshe IBB ya bayyana rashin mutanen a matsayin babbar rashi ga Najeriya, tare da fatan Allah ya jikansu, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel