Shugabanin kungiyar masoya Buhari sun kai ziyara fadar gwamnati, kalli hotuna
Shugabanin kungiyar magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari na "Buhari Support Group" sun kai masa ziyarar ban girma fadar Aso Rock dake babban birnin tarayya Abuja a yau 20 ga watan Yulin shekarar 2018.
Tawagar magaya bayan shugaban kasar sun kai ziyarar ne karkashin jagorancin Direkta Janar na kungiyar, Umaru Dembo.
DUBA WANNAN: Dalilin da yasa ake yawan samun afkuwar hatsari a titin Badagry zuwa Seme - Hukumar FRSC
Wannan ziyara tasu tana zuwa ne a lokacin da su kuma Kungiyar Dattawan Arewa tare da wasu kungiyoyin suke sukan shugaban kasar inda suka ce gwamnatinsa bata daukan matakan da suka dace wajen kawo karshen kashe-kashe da akeyi a wasu sassan kasar.
Sai dai a yau Juma'a, fadar shugaban kasar ta mayar musu da martani inda ta shawarci 'yan Najeriya suyi watsi da batun Dattijan arewa.
Fadan shugaban kasar tace tarin mutane ne kawai masu son kansu ba wai al'ummar Najeriya ba kuma korafin da su keyi ma duk na yaudara ce kamar hawayen kada.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng