Dattijan Arewa sun fiye son kansu, kunya ce ta ishe su suke so su tade kafar Buhari - Fadar shugaban kasa

Dattijan Arewa sun fiye son kansu, kunya ce ta ishe su suke so su tade kafar Buhari - Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa tayi kaca-kaca da wasu dattawan Arewa da wasu kungiyoyi da suka fitar da wata sanarwa inda su kayi ikirarin cewa shugaba Muhammadu Buhari baya daukan matakan da suka dace game da harkar tsaro a kasar.

Fadar shugaban kasar tayi kira ga 'yan Najeriya suyi watsi da batun dattawan inda tace borin kunya ce irin da yaudara irin ta mutanen da kawai kansu suke so ba wai cigaban al'umma ba.

Wannan martanin da fito ne cikin wata sanarwa da hadimin shugaba Muhammadu Buhari kan fannin kafafen yadda labarai, Malam Garba Shehu, ya fitar a yau Juma'a.

Yace shugabanin kawai suna korafi ne saboda gwamnatin Buhari ta ware su a gefe kuma ta dakile hanyoyin da suka saba bi suna azirta kawunansu da dukiyoyin kasa.

Dattijan Arewa sun fiye son kansu, kunya ce ta ishe su suke so su tade kafar Buhari - Aso Rock
Dattijan Arewa sun fiye son kansu, kunya ce ta ishe su suke so su tade kafar Buhari - Aso Rock

DUBA WANNAN: Ya sake ta wai haihuwa take kamar zomo, bayan ta haifa masa yara shida

Dattawan sunyi korafi kan kamun ludayin gwamnatin Buhari game da batun tsaron ne a wata sakon baya taro da Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) da wasu shugabanin kungiyoyi suka gudanar don tattauna matsalolin kasar.

Sai dai, fadar shugaban kasar ta bukaci 'yan Najeriya suyi watsi da 'taron marasa son gaskiya da suke son kawo wa jam'iyyar APC cikas musamman yanzu ta jam'iyyar ke kara buwaya a sassan kasar kuma take gab da nasara a zaben 2019."

Shehu yace duk wanda ke ikirarin cewa shugaba Muhammadu Buhari bai dauki mataki game da kashe-kashen da akeyi ba ya duba sakon da Femi Adesina ya fitar mai taken "Combating Insecurity in the Country: Lest we Forget" cikin kwana-kwanan nan inda ya zayyana dukkan matakan da shugaban kasa ya dauka don inganta tsaro.

A cikin sakon, Adesina ya lissafo dukkan atisayen soji da gwamnati ta kaddamar a jihohin Najeriya da dama wanda suka hada da 'Ayem Akpatuma' don magance satar mutane, rikcin makiyaya/manoma da sauransu a jihohin Benue, Taraba, Kogi, Nasarawa, Niger da Kaduna.

Ya kuma ce gwamnati ta amince kafa sabbin battaliya soji da rundunar yan sanda a Birnin Gwari a jihar Kaduna da wasu kuma a jihar Filato.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164