Jigo a APC ya nemi afuwar kotun koli bisa zarginta da karbar na goro

Jigo a APC ya nemi afuwar kotun koli bisa zarginta da karbar na goro

Wani shugaba a jam'iyyar APC, Joe Igbokwe, ya nemi afuwar kan zargin da ya yi na cewa Gwamna Wike ya saye alkalan kotun don su bashi nasara a shari'ar zaben gwamna a jihar Rivers da aka gudanar a shekarar 2015.

Igbokwe, wanda shine sakataren yadda labarai na APC reshen jihar Legas ya yi rubutu a shafinsa na Facebook ranar Litinin, inda yace gwamna Nyesome Wike na jihar Rivers ne ya bawa alkalan kotun kolin don ya samu nasarar a shari'ar zaben gwamna ta 2015.

"Babu shakka Wike ba zai iya cigaba da kashe mutane a jihar Ribas ba ko kuma ya bawa alkalan kotun koli cin hanci. Hakan ba zata taba faruwa a karkashin mulkin shugaba Buhari ba," kamar yadda ya fadi a dandalin sada zumuntan.

Jigo a APC ya nemi afuwar kotun koli bisa zarginta da karbar na goro

Jigo a APC ya nemi afuwar kotun koli bisa zarginta da karbar na goro

Wannan kalaman nasa ne yasa gwamnatin Rivers ta bashi wa'addin kwanaki 7 ya ambaci sunayen alkalan da ya yi ikirarin an bawa cin hanci ko kuma a gurfanar dashi gaban kuliya.

DUBA WANNAN: Ya sake ta wai haihuwa take kamar zomo, bayan ta haifa masa yara shida

Kwanaki hudu bayan wa'addin da aka bashi, jigon na jam'iyyar APC ya janye abinda ya fada kuma ya nemi ayi masa afuwa.

"Ina son amfani da wannan damar don sanar da al'umma cewa na janye abinda na fada kwanakin baya inda nayi ikirarin cewa an bawa wasu alkalan kotun koli cin hanci a game da shari'ar zaben gwamna na 2015 a jihar Rivers.

"Ba niya ta bane wulakanta kotu da alkalanta saboda ina daraja su sosai.

"Kuskure ce kuma zan dauki duk wata hukunci da zata biyo baya. Banda hujjan fadin hakan, ra'ayi na ne kawai. Ina neman afuwar duk wadanda abin ya shafa kuma nayi alkawarin ba zan sake yin haka ba a gaba. Dan adam dai bai wuce kuskure ba!," Kamar yadda Mr Igbokwe ya rubuta a Facebook a yau Juma'a.

Sai dai duk da hakan gwamna Wike yace dole ya rubuta takardan neman afuwa ya kai kotu kuma sai ya janye zargin kisa da yace gwamnan ya yi kafin gwamnati tasan matakin da zata dauka a kansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel