Tsaleliyar budurwa ta bayyana yadda dan uwanta ya tsiyayar mata da ido daya

Tsaleliyar budurwa ta bayyana yadda dan uwanta ya tsiyayar mata da ido daya

- Budurwar da yayana ya harba sau biyar ya fasa mata ido ta yafe masa

- Sannan a kotu da aka yanke masa hukuncin shekaru 45 a kurkuku ta tausaya masa hakan tasa alkali ya rage su zuwa 10

Wata matashiyar zankadediyar budurwa ta bayyana yafiyarta ga dan uwanta bisa laifin da ya yi mata harbi har sau biyar wanda haka ya zama sanadin rabata da idonta guda daya a shekarar 2016, a sakamakon mayen giya da yake ciki.

Budurwar ta bayyana cewa ta rasa Idon na ta ne, a lokacin da dan uwan nata y ke cikin mayen giya, inda ya yi mata harbi har guda biyar.

KU KARANTA: Ba zan iya ba: Wani Saurayi ya rabu da Budurwar sa saboda ‘dan karen kazantar ta

Ta ce bayan ya yi min wannan harbin ne aka garzaya da ni zuwa asibiti domin ceto rayuwata, inda ta samu makwanni tana karbar magani. Sannan ta kara da cewa "Bayan da na farfado daga dogon suman da na yi, sai na ji jikina ya yi min nauyi tare kuma da jin idona baya iya gani yadda ya kamata"

Bayan ya aikata wannan danyen laifin, sai kotu ta daure shi kimanin shekaru arba'in da biyar a gidan yari, amma saboda tausayinsa da ta nuna mai shari’ar ya rage zuwa goma.

Daga nan ne ta bayyana cewa duk da irin laifin da dan uwan nata ya aikata mata, ta yafe masa domin tana da kyakykyawan zaton ya zama mutum nagari yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng