An zo wajen: Za’a fara biyan sabbin yan N-Power albashinsu daga watan Agusta

An zo wajen: Za’a fara biyan sabbin yan N-Power albashinsu daga watan Agusta

Tsarin tallafa ma matasa tare da rage ma yan Najeriya radadin talauci, N-Power da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kirkiro na cigaba da samun tagomashi, inda daga watan Agusta mai zuwa gwamnatin tarayya za ta fara biyan sabbin yan N-Power albashinsu.

Legit.ng ta ruwaito wani hadimin shugaba Buhari, Ismaeel Ahmad ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 19 ga watan Yuli, inda yace daga daya ga watan Agusta wadanda aka dauka zasu fara aiki a dukkanin bangarorin da aka daukesu.

KU KARANTA:Gwamna El-Rufai ya fara shirin 2019, ya nada sabbin Sojojin yakin neman zabe

Hadimin yace a ranar 20 ga watan Yuli za’a aika ma dukkanin jami’an dake kula da N-Power a jihohi sunayen mutanen da aka dauka a jihohinsu, da rabe raben kananan hukumomin da suka fito, don turasu ga hukumomin hadin gwiwa da zasu aikasu inda zasu fara aiki.

An zo wajen: Za’a fara biyan sabbin yan N-Power albashinsu daga watan Agusta
N-Power

Wasu daga ciki hukumomin hadin gwiwar sun hada da hukumomin ilimin bai daya na jihohi, hukumomin ilimin yaki da jahilci, hukumomin ilimin makiyaya, sashen cigaban noma, da kuma cibiyoyin karbar magani a mataki na farko.

Fadar shugaban kasa ta umarci dukkanin jihohin Najeriya su mayar da sunayen mutanen da suka tura tare da inda suka turasu ga ofishin N-Power dake Abuja zuwa ranar 3 ga watan Agusta, haka zalika ana bukatar dukkanin wadanda aka dauka dasu daura takarda dake dauke da sa hannunsu don bayyana da ranar da suka fara aiki, da haka ne zasu fara samun albashinsu daga watan Agusta.

Daga karshe hadimin yana kara jaddada ma mutanen dake cin gajiyar N-Power cewa zasu ci moriyar wannan tsari ne na tsawon shekaru biyu kacal, daga watan Agustan shekarar 2018, zuwa ranat 31 ga watan Yuli na shekarar 2020.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng