EFCC zata hada karfi da karfe da kasar Ingila wurin kawo karshen cin hanci a Najeriya
Kasar Birtaniya zata tallafawa hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kayan aiki na fasahar zamani wurin ganin an kawo karshen cin hanci a kasar nan
Kasar Birtaniya zata tallafawa hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kayan aiki na fasahar zamani wurin ganin an kawo karshen cin hanci a kasar nan.
Paddy Kerr, shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na kasar Birtaniya, ta cibiyar yaki da ta'addanci a Najeriya, shine ya sanar da hakan, inda yace zasu tallafawa Najeriya wurin yaki da cin hanci da rashawa, wanda ya hada da tallafa mata da kayayayyakin fasahar zamani.
DUBA WANNAN: Wasu 'yan fashi sun asirce jami'an 'yan sanda sun gudu
Kayayyakin fasahar zamanin da hukumar yaki da cin hanci da rashawan ke amfani dasu sun kasance abun tunkaho ga kowacce cibiyar tabbatar da doka.
Wannan yunkurin ya biyo bayan kokarin yaki da cin hanci da rashawa da shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari yake yi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng