Ya sake ta wai haihuwa take kamar zomo, bayan ta haifa masa yara shida

Ya sake ta wai haihuwa take kamar zomo, bayan ta haifa masa yara shida

Wani magidanci mai shekaru 39, Micheal Ayinde ya maka mai dakinsa a kotu inda yake korafi cewa ta cika haihuwar yara barkatai. Ayinde ya kwashe shekaru tara yana zaman aure da matarsa Glory.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa Alkalin kotun Customary dake Igando, Akin Akinniyi, ya yanke hukuncin cewa rashin amsa gayyatar kotu da Glory tayi babban alama ce dake nuna cewa auren ya samu matsala sosai.

Ya sake ta wai haihuwa take kamar zomo, bayan ta haifa masa yara shida
Ya sake ta wai haihuwa take kamar zomo, bayan ta haifa masa yara shida
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jinin da ake zubarwa a Najeriya ya yiwa - Sarkin muslmi ya koka

Ya ce: "Tun fara shari'ar, wanda aka kawo kararta (Glory) bata hallarci zaman kotun ba. Haka yasa kotu ta zartar da hukuncin raba aure tsakanin Michael Ayinde da Glory. Kowa yana da ikon ya kama gabansa ba tare da cin zarafi ko cin mutuncin juna ba."

An ruwaito cewa Ayinde ya shaida wa kotu cewa matarsa tana ta haifar yara barkatai duk da cewa ta san halin da kasar ke ciki na wuyar rayuwa. Ya kara da cewa a yanzu suna da yara shida.

Kalamansa: "Allah ya baka nasara, mai dakina tana son ta kashe ni da yara. Tana haihuwa kamar zomo. Cikin shekaru tara ta haifi yara shida. An sallame ta daga aiki saboda ta sake daukan ciki bayan ta dawo daga hutun haihuwa.

"Bayan ta haifi yaron mu na hudu, na bukaci ta tafi asibiti domin mu kayyade iyali amma daga baya da cire na'urar kayyade iyalin ba tare da sani na ba. Bayan watanni kadan lokacin ta tafi gidan iyayenta sai ta aiko min sakontes cewa tana da ciki. Bata dawo ba sai bayan data haihu kuma akayi suna."

Ya kuma kara da cewa a ranar 24 ga watan Disambar 2016, Glory ta tafi gidan iyayenta inda ta kira ta fada masa tana da ciki amma bai amince ta dawo gidansa ba. Ya tilasta ta tsayawa gidan iyayenta har sai ta haihu kuma anyi suna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164