Yadda zaku iya gane jabun magungunan gona
Daya daga cikin abinda ke haifar wa manoma asara da samun karancin amfanin gona shine amfani da taki da magungunan kwari na jabu ko wadanda aka yiwa hadi da wasu abubuwan da ke gurbatasu.
Manoma da yawa suna kashe makuden kudade wajen sayan taki da magungunan kwari kuma duk da haka basu samun wasu amfanin gona masu auki da inganci.
Hakan yasa sau da yawa za kaji manoma suna kokawa kan yadda magungunan da suka saya basu biya musu bukata.
DUBA WANNAN: An yankewa wata hukuncin daurin shekaru 3 bayan ta yiwa wata kaca-kaca da reza
Saboda kauce wa wannan matsalar, mun zakulo muku wasu hanyoyin da za'a iya bi wajen banbance jabu da kayayakin aikin gona masu nagarta.
1) Araha
Shin abinda zaka siya tayi araha ta yawa? Ya kamata manoma su rika bincike sosai kafin su siya magunguna musamman wanda suka ji farashin ya yi araha da yawa, su duba tambarin kamfanin kafin su saya.
"Idan ka lura farashin ya yi araha sosai, ka tambayi dalilin ka inda ya sayo kayan," kamar yadda mujallar manoma ta wallafa.
2) Tabbatar a rufe yake kuma tambarin ya yi dai-dai da na kamfanin
Mujallar ta manoma kuma ta shawarci manoma su kasance sun san yadda tambarin kamfanonin dake sarrafa kayayakin aikin noma suke yadda zasu iya banbance su da jabu ta hnayar launi da sauran alamomi.
Ya kuma kamata manomi ya tabbatar duk abinda zai siya a rufe take daga kamfani, ma'ana ba'a bude an rage ko kara wani abu ba.
Idan kuma manomi zai siya kayayakin da yawa ne, ya kamata ya duba sunan dake recipt dinsa ya tabbatar ya yi dai-dai da abinda aka bashi .
3) Yin sayaya daga amintatun diloli
Abu na karshe shine yana da kyau manoma su tabbatar cewa suna sayan magungunan da sauran kayayakinsu daga amintatun diloli saboda yana da wahala su saya jabu a irin wannan wurare.
Baya ga haka, amintatun diloli suna bawa manoma shawarwari bayan sun saya kaya a wajensu kan yadda za'ayi amfani da kayayakin don samun biyan bukata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng