Kyawun tafiya: Tsarabar ayyukan cigaba 3 da Buhari ya dawo da su daga kasar Holand
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a jiya ne shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo gida bayan kammala ziyarar aiki ta kwanaki uku da ya kai kasar Holand dake tarayyar turai.
A ziyarar dai mun samu cewa ya halarci bikin cikar kotun kasa-da-kasa dake a kasar shekaru ashirin da kafiwa inda ya gabatar da kasida mai daukar hankali.
KU KARANTA: Wasu 'yan Arewa sun caccaki Atiku
Legit.ng sai dai ta samu cewa ba wannan ne kadai ba domin kuwa shugaban kasar ya samo ma kasar tsarabar ayyukan cigaba akalla uku.
1. Yanzu babban kamfanin nan dake samar da kayatattun kayan mata na Vlisco zai kafa kamfani a Najeriya.
2. Haka ma babban kamfanin samar da madara na Friesland Campina shima ya kuduri aniyar zuwa Najeriya don kafa kamfani.
3. Haka zalika kamfanin nan fitacce na Cownexxion da ya shahara wajen kiwon shanu na zamani a duniya shima ya ce zai kwance hajar sa a Najeriya
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng