Gwamnatin Buhari ta kafa tarihi: Zaman majalisar zartarwa bai samu yiwuwa ba a karo na 6 a jere
- Gwamnatin tarayya bata samu damar gudanar da taron majalisar zartarwa na mako-mako da ta saba yi ba a karo na shida a jere
- Ranar 20 ga watan Yuni ce lokaci na karshe da gwamnatin tarayya ta gudanar da taron majalisar zartarwa
- Duk da fadar shugaban kasa bata fitar da wata sanarwa dangane da dalilin rashin yin taron ba, rahotanni sun bayyana an soke zaman da ya kamata a yi yau ne jiya da daddare
A karo na tun bayan hawan Buhari mulkin Najeriya a shekarar 2015, gwamnatin tarayya bata samu damar gudanar da taron majalisar zartarwa na mako-mako da ta saba yi ba a karo na shida a jere.
Ranar 20 ga watan Yuni ce lokaci na karshe da gwamnatin tarayya ta gudanar da taron majalisar zartarwa, lokacin da shugaba ya saka hannu kan kasafin kudin shekarar nan kafin shiga hutun sallah.
Duk da fadar shugaban kasa bata fitar da wata sanarwa dangane da dalilin rashin yin taron ba, jaridar Vanguard ta rawaito cewar an soke zaman da ya kamata a yi yau ne jiya da daddare.
DUBA WANNAN:
Wata majiya a fadar shugaban kasa, da bata yarda a ambaci suna ba, ta bayyana cewar taron na wannan mako ba zai yiwuwa bane saboda shugaba Buhari baya kasar, sannan mataimakinsa ya kai ziyara jihohin Katsina da Sokoto domin jajantawa mutanen da ambaliyar ruwa ta yiwa barna.
Ana zaman majalisar zartarwa ne ranar Laraba ta kowanne mako domin tattauna muhimman batutuwan gwamnati da kuma daukan matakai ko yanke shawara a kan dukkan wani abu da ya shafi kasa bakidaya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng