Manyan Sarakunan gargajiya a Najeriya sun gudanar da wani babban taro a Abuja

Manyan Sarakunan gargajiya a Najeriya sun gudanar da wani babban taro a Abuja

A yau, Laraba, 18 ga watan Yuli ne mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya halarci taron kara ma juna sani na manyan Sarakunan gargajiyar Najeriya da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja.

Legit.ng ta ruwaito Mataimakin shugaba Osinbajo ne ya kaddamar da taron, mai taken sake dawo da martabar Najeriya, wanda ya gudana a dakin taro na gidan karrama yan Najeriya dake Abuja.

KU KARANTA: Hukumar Hisbah ta yi ram da Almajirai 500 dake yawon bara a garin Kano

Manyan Sarakunan gargajiya a Najeriya sun gudanar da wani babban taro a Abuja
Manyan Sarakunan gargajiya

Taron ya samu halartar sarakuna daga sassan Najeriya, kuma an yi shi ne a karkashin jagorancin shugaban majalisar sarakunan gargajiya na Najeriya, mai martaba Emmanuel Ekemejewa Siseso Abe I.

A wani labarin kuma, Osinbajo ya kai ziyarar jaje ga al’ummar karamar hukumar Jibia na jihar Katsina, sakamon ibtila’in ambaliya da ya fada musu a sanadiyyar ruwan sama da ka sha kamar da bakin kwarya a dare Litinin wanda ya halaka mutane da dama tare da barnata dukiyoyi.

Manyan Sarakunan gargajiya a Najeriya sun gudanar da wani babban taro a Abuja
Manyan Sarakunan gargajiya

A yayin ziyarar tasa, Osinbajo ya bayana alhininsa da na Maigidansa shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda yace gwamnatin taraya za ta hada hannu da gwamnatin jihar Katsina don tallafa ma wadanda abin ya shafa, kuma ya yi alkawarin mayar da dukkanin mutanen da abin ya shafa gidajensu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel