Rikicin Makiyaya: An kashe sama da mutum 500 a Filato, Nasarawa, Kogi, da Benuwai
Labarin da mu ka samu kwanakin baya bai da dadin ji ko kadan inda aka bayyana mana cewa sama da mutum 500 sun zama babu a cikin shekarar nan a sanadiyyar rikicin Makiyaya da Mazauna.
Jaridar Daily Trust tayi bincike inda ta bayyana cewa an hallaka mutane 579 a Jihohin Filato da Nasarawa da Kogi da kuma Jihar Benuwai da ke Arewa maso Tsakiyar Najeriya. An kashe wannan mutane ne duk a shekarar bana.
Daga watan Junairu zuwa watan Jiya na Yuni, sama da mutum 500 su ka bakunci lahira a dalilin rikicin Makiyaya da ‘Yan Gari a Jihohin Arewan da mu ka lissafo. Daga cikin wanda su ka mutu, har da manoma da malaman addini da matafiya.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gana da manyan hafsoshin sojin kasa kan tsaro
Tun kwanaki ne Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto mai ban tsoro. Daga cikin wadanda su ka rasa rayukan na su har da wani Mai gari a Yankin na Arewa ta tsakiya. Abin har ya kai an rasa Sojoji fiye da 25 na Kasar nan a Juhar Benuwai.
Bayan kashe-kashen mutane, ana kuma samun satar shanu da ake yi a Yankin. A shekarar nan dai an sace shanu kusan 100 a Jihar Kogi. Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Muhammed Hussaini ya nemi Gwamnatin Buhari ta yi abin da ya dace.
Jiya kun ji wani yadda Jakadan kasar waje a Najeriya ya karyata Shugaba Buhari na cewa da hannun Mutanen waje a wajen kashe-kashen. Jakadan na Faransa yace sam babu ruwan ‘Yan kasar waje a wajen kashe-kashen da ake yi a Arewacin Najeriya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng