Hanyoyi biyar da suka fi janyo haddura a Najeriya

Hanyoyi biyar da suka fi janyo haddura a Najeriya

Hatsarin mota babban abu ne da ya dade yana ciwa 'yan Najeriya tuwo a kwarya, kusan ko wace rana zaka rika samun labarun hatsarin motoci dake faruwa a titunan Najeriya. Alkalumar Cibiyar kididiga ta kasa (NBS) ya nuna cewa an samu hatsarin mota 11,363 a 2016 wanda ya yi sanadiyar rasuwar mutane 5,053.

Kamar yadda kowa ya sani rashin kyawun hanyoyi yana daya daga cikin abubuwan dake janyo hadurra a titunan Najeriya, hakan yasa muka tattaro muku tittuna 7 mafi hadari a Najeriya.

1) Titin Kaduna-Abuja

Hanyoyi biyar da suka fi janyo haddura a Najeriya

Hanyoyi biyar da suka fi janyo haddura a Najeriya

Duk da cewa tittin Kaduna zuwa Abuja shine ya sada babban birnin Tarayya Abuja da jihohin Arewa masu yawa, har yanzu akwai daruruwan ramuka a titin. Idan ba'a manta ba a hanyar ce wata Hummer Bus dauke da fasinjoji 18 tayi hatsari inda 14 suka kone kurmus.

DUBA WANNAN: An bayar da kiyasin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Katsina

2) Titin Abuja-Lokoja-Okene-Kabba

Hanyoyi biyar da suka fi janyo haddura a Najeriya

Hanyoyi biyar da suka fi janyo haddura a Najeriya

Wannan hnayar tayi kaurin suna wajen matafiya saboda yawan hatsari da ake samu a hanyar. Idan mutum na son zuwa Abuja ko Ondo da sauran jihohin Kudu maso yammacin Najeriya, dole sai yabi ta hanyar Lokoja-Okene kuma hanyar ta lalace sosai ka kuma 'yan fashi da makami.

3) Titin Otukpo-Otukpa dake Makurdi

Hanyoyi biyar da suka fi janyo haddura a Najeriya

Hanyoyi biyar da suka fi janyo haddura a Najeriya

"Ga wadanda suka saba bin wannan hanyar, duk lokacin da suka karato titin Otukpa-Otukpo suna cike da faduwar gaba saboda rashin sanin abinda ka iya faruwa" kamar yadda wani marubuci ya wallafa.

Baya ga zaizayar kasa da ramuka a titin, hanyar tayi kaurin suna saboda fashi da makami da ake a hanyar.

4) Titin Legas-Sagamu-Ore-Benin

Hanyoyi biyar da suka fi janyo haddura a Najeriya

Hanyoyi biyar da suka fi janyo haddura a Najeriya

Wannan titin ya kasance titi guda da ya dade yana ciwa gwamnatocin da suka shude a shekaru 20 da suka wuce tuwo a kwarya, inji wani mai nazarin al'amurran yau da kullum. Ya fadi hakan ne saboda irin rashin kyawun hanyar.

Idan ba kwararen direba ba, bin wannan hanyar ba karamin hadari bane duba da yadda akwai manyan ramuka da ka iya janyo hadari ko fashewar taya, ka kuma masu fyade da yan fashi dake jira motar ka ta lalace su far maka.

5) Titin Legas-Ibadan

Hanyoyi biyar da suka fi janyo haddura a Najeriya

Hanyoyi biyar da suka fi janyo haddura a Najeriya

An gina wannan hanyar ce tun 1974 kuma tsawon ta ya kai kilomita 120 amma a halin yanzu hanyar da lalace sosai duk ta fashe. Saboda haka ana yawan samun haddura a hanyar kuma galibi direbobin tankar dankon man fetur ne suka fi janyo hatsarin saboda irin gudu da suke yi a hanyar.

A kididgar da FRSC ta fitar, an samu haddura 2,075 wanda ya yi sanadiyar rasuwar mutane 775 a hanyar a shekarar 2012.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel