Yanzu-Yanzu: Tsohon Alkalin Alkalai na kasa, Katsina-Alu ya rasu
Tsohon Babban Alkalin kotun koli ta Najeriya, Aloysius Iyorgyer Katsina-Alu ya rasu.
Marigayin ya rasu yana da shekaru 76 kuma da yana raye zai cika shekaru 77 wata mai zuwa.
Katsina-Alu dan asalin jihar Benue ne kuma shi ya gaji Idris Legbo Kutigi a matsayin babban Alkalin kotun koli ta kasa a watan Disambar 2009 kuma ya kammala wa'adinsa a watan Augustan 2011.
Sahara reporters ta wallafa cewa majiyarta ta tabbar da rasuwar Katsina-Alu a yau Laraba inda tace rasuwar ya girgiza al'ummar Tiv da kasa baki daya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng