Basabamba: Sheikh Gumi ya jinjina ma gwamnatin Buhari a fannoni guda 3

Basabamba: Sheikh Gumi ya jinjina ma gwamnatin Buhari a fannoni guda 3

Fitaccen Malamin nan dake jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi wanda yayi kaurin suna wajen sukar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, tare da jagoran gwamnatin kansa Buhari, ya bayyana cewa akwai abubuwan alheri game da gwamnatin Buhari.

Gumi ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da gidan rediyon muryar Amurka, VOA Hausa, inda yace akwai alkairai da gwamnatin Buhari, musamman a wasu fannoni guda uku da yace gwamnatin ta yi rawar gani, don haka ta cancanci yabo.

KU KARANTA: Yan bindiga yi garkuwa da wani Basarake, sun bindiga Dansa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wadannan fannoni guda uku da Gumi ya tabbatar da cewa gwamnatin Buhari ta yi rawar gani sun hada da sha’anin noma, yaki da kungiyar ta’addanci na Boko Haram da kuma rage ma daliban jami’a kudin makaranta.

“Gwamnatinnan ta yi abin kirki a wajen baiwa manoma tallafin don inganta noma, haka nan ta yi kokari matuka a yakin da take yi da Boko Haram, sa’annan na yaba da matakin rage ma daliban jami’a kudin makaranta.” Inji shi.

Sai dai da aka tambayi Malamin akan menene matsalar gwamnatin Buhari, sai ya kada baki yace: “Matsalar rarrabuwar kai a tsakanin yan Najeriya, don kuwa ko kawunan Musulman Arewa ma ba a hade yake ba, balle ma nay an Najeriya, kuma wannan yafi duk wani abinda za ka yi ma jama’a.”

Daga karshe Gumi ya tabbatar da cewa magoya bayan shugaba Buhari dakikai ne, inda yace ba shi ya fara fadin haka ba, “Ai Buharin da kansa ne ya fara fadin haka a wata ziyara da ya kai Turai, inda yace kasha sittin na matasan Najeriya malalata ne, kuma basu da ilimi, toh ai da su yake.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel