Shugaba Buhari ya kai ziyarar gani da ido zuwa wata Matatar mai ta zamani (Hotuna)
A yayin ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai kasar Netherland, an zazzagaya da shi wasu wurare a kasar don gane ma idanunsa irin cigaban da kasar ta samu, da nufin ko zai kwatanta kwatankwacin cigaban a gida Najeriya.
A ranar Litinin, 16 ga watan Yuli ne shugaba Buhari ya tafi kasar Netherland, bayan samun gayyata dsaga babbar kotun Duniya dake hukunta manyan laifuka, ICC, don halartar taron taron cika shekaru ashirin da samar da dokar kafata.
KU KARANTA: Kaico! Wani Matashi ya daddatsa Mahaifiyarsa gunduwa gunduwa
Da wannan ziyarar da ya kai, Shugaba Buhari ya kafa tarihi a matsayin shugaban kasa daya tilo daga nahiyar Afirka da Kotun ICC ta taba gayyata irin wannan taro, wanda a yayin taron an baiwa Buhari damar gabatar da kasida a gaban Alkalan Kotunan gaba daya.
A bayan wannan taro ne kuma sai aka zagaya da Buhari zuwa tashar jirgin ruwa na birnin Rotterdam don gane ma idanunsa cigaban tashar ta samu, haka zalika an zagaya da shi matatar main a zamani mallakin kamfanin Shell Pernis.
A yayin wannan zagaye zagaye, Buhari ya samu rakiyar shugaban hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa na Najeriya, Hadiza Bala Usman, gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu da shugaban tashar jirgin ruwa na Rotterdam, Allard Castelein.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng