Kotu ta dage sauraron karar Jonah Jang sai baba ta gani
Kotu ta dage shari'ar tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, wanda ake zargi da cinye Naira biliyan 6.3 zuwa 30 ga watan Oktoban wannan shekarar
Kotu ta dage shari'ar tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, wanda ake zargi da cinye Naira biliyan 6.3 zuwa 30 ga watan Oktoban wannan shekarar.
Jang, sanata ne mai ci a yanzu kuma yana gaban shari'a ne karkashin mai shari'a Daniel Longji na babbar kotun jihar Filato a bisa zargin shi da ake da laifuka 12 da suka hada da barnatar da dukiyar al'umma.
DUBA WANNAN: Kalli dalilan da suke sanya samarin mu shiga shaye - shaye
A tare da shi akwai daya daga cikin ma'aikatan ofishin Sakataren Gwamnatin jihar, Yusuf Gyang Pam, wanda shima ake zargin shi da amfani da kujerar shi gurin azurta kanshi da Naira miliyan 11.5.
Jang dai ya almubazzarantar da wasu kudade na musamman da babban bankin Najeriya ta tura jihar shi don rabawa kanana da matsakaitan kasuwanci domin bunkasa su, ana saura wata biyu ya sauka daga kujerar shi ta gwamnan jihar a shekarar 2015.
Shari'ar da aka yanke sauraron ta a yau 17 ga watan Yuli, an yanke hukuncin dage ta ne saboda shaidun masu karar basu halarci kotun ba.
Lauyan masu karar ya roki mai shari'a da ya dage sauraron karar saboda rashin samun damar kawo shaidar zuwa kotun sakamakon rashin tsaro a jihar.
An dage shari'ar tare da fatan zaman lafiya da kwanciyar hankali zasu dawo jihar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng