Baku san aikinku ba: Buhari ya watsa ma yan majalisu kasa a ido akan wasu bukatu 4 da suka mika masa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya watsa ma yan majalisun dokokin Najeriya su dari hudu da sittin d tara, 469, kasa a idanuwansu bayan yaki amincewa ya sanya hannu akan wasu kuduri guda hudu da suka aike masa dasu don ya sanya musu hannu, su zama doka.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito kudurorin suna hada da kudurin dokar kisan kai na shekarar 2018, kudurin dokar hukumar kare hakkin yara 2018, kudurin dokar bada bashi ga manoma 2018, da kuma kudurin dokar samar da tabbataccen kudin tara na 2018.
KU KARANTA:
Buhari ya aika ma shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki dalilansa na kin sanya hannu kan wadannan kudurori a cikin wata wasika da Sarakin ya karata a bainar majalisar a ranar Talata, 17 ga watan Yuli.
Hujjar da BUhari ya bayar game da kin amincewa da kafa hukumar kare hakkin yara itace, a cewarsa ma’aikatar kula da mata ne ke daukar wannan dawainiya, don haka bai ga dalilin kafa wata hukumar dta daban ba, asarar kudi ce kawai, inji Buhari.
Game da samar da tabbataccen kudin tara na Kotuna kuwa, Buhari cewa yayi yan majalisun basu tantance aikin kudurin ba, kuma ma dokar za ta ci karo da tsarin sanya kudaden tara da dokokin Najeriya suka tanadar.
Haka zalika dangane da dokar bada bashi ga manoma kuwa, Buhari yace karin kudaden bashi ga manoma zuwa naira biliyan hamsin ba zai yiwu ba, “Amma idan kuka gyara wannan kudurin, zan sanya mata hannu.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng