Jami'an 'yan sanda sun kama wasu shugabannin kungiyar asiri guda 2
- An kama su suna yiwa 'yan mata fyade sannan kuma su sakasu a kungiyar asirin
- Jami'an 'yan sandan sunyi nasarar biyu daga cikin shugabannin kungiyar
A ranar Talatar nan ne mai magana da yawun hukumar 'yan sanda dake jihar Enugu SP Ebere Amaraizu ya bayyana samun nasarar su akan yaki da kungiyoyin matsafa. Inda ya shaidawa manema labarai cewar jami'an su sun samu nasarar cafke mutane biyu wadanda suke manya daga cikin 'yan kungiyar asirin.
Wadanda ake zargin sun hada da Emmanuel Enuh dan shekara 18 da Chukwuebuka Egwu dan 18. Yace sun dade suna aikata wannan laifi kafin a samu nasarar cafke su.
DUBA WANNAN: Adeosun: Har yanzu hukumar NYSC taki gabatar da wata kwakkwarar shaida
Jami'in dan sandan ya kara da cewa wadanda ake zargin suna fara yiwa mata fyade kafin su sanyasu a cikin kungiyar ta mata wadda sukayi wa lakabi da WHITE ANGELS CULT wanda mafi yawansu yan makarantar sakandire ne.
Daya daga cikin wadanda ake zargin Onuh yace shi mai aikin famfo ne inda yake zaune da yar uwarshi a Mount street a jihar Enugu.
Yace ya shiga kungiyar ne a shekarar 2015 lokacin yana aji daya a makarantar sakandire, daganan ya fara shiga wani daji dake kusa da makarantar tasu.
"Kungiyar tayimin alkawarin bani kariya a koda yaushe sannan zan zama shahararre a yankinmu, aduk lokacin da nake bukatar mace zan samu, zuwa yanzu nayi nadama fitar shine matsalar," inji Onuh.
Yan mata masu sha'awar shiga kungiyar anayi musu fyade kafin su shiga.
Amaraizu yace ana cigaba da zurfafa bincike akan lamarin.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng