Cin amana ruwa ruwa: Yadda Maigadi ya tafka ma Maigidansa mummunar ta’asa

Cin amana ruwa ruwa: Yadda Maigadi ya tafka ma Maigidansa mummunar ta’asa

Rundunar Yansandan jihar Neja ta sanar da damke wuyar wasu miyagun mutane bata gari da suka yi awon gaba da wani karamin yaro mai shekaru goma, Afdal Haddi a garin Dutse Kura, dake cikin garin Minna, na jihar, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito miyagun mutanen sun hada da Yusha’u Bala, Maigadin gidasu Afdal, dake unguwar GRA Minna wanda ya hada baki da wani matashi mai shekaru Ashirin, Sale Bala.

KU KARANTA:

Bayan sun yi garkuwa da Afdal, sai Sale da Yushau suka nemi iyayen Afdal su basu kudin fansa da ya kai naira dubu dari da hamsin, 150,000, kafin su sake shi.

Cin amana ruwa ruwa: Yadda Maigadi ya tafka ma Maigidansa mummunar ta’asa
Masu laifin

A nasa jawabin, Yushau Bala ya bayyana ma Yansanda cewar sun shirya sace Afdal ne da nufin karbar kudin fansa don su inganta rayuwarsu, sakamakon sun kwashe shekaru aru aru suna gadi amma basu tara komai ba, don haka sun gaji da wahalar gadi.

“Kudin fansar da muke nema, N150,000 ba wani abu bane idan aka kwatanta shi da makudan kudaden da wasu barayin mutane suke nema ba, don haka mun shiga harkar ne don mu samu yan kudin da zasu rike mu, mu saki sana’ar gadi.

“Ina fata Yansanda zasu yafe mana, saboda ban san yadda aka yi ma muka shirya sace wannan yaron Maigidan anwa ba.” Inji shi.

Daga karshe Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Muhammad Abubakar ya bayyana cewa zasu shigar da barayin biyu kara gaban kuliya manta sabo, da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng