An kashe yan sanda 4 sannan aka kona su kurmus a motar sintiri a Edo

An kashe yan sanda 4 sannan aka kona su kurmus a motar sintiri a Edo

Wasu mutane da ba’a san ko su wanene ba sun kashe jami’an yan sanda hudu dake aiki da hedkwatar yan sanda na Sabongida-Ora, sannan suka kona su kurmus a motar sintiri a karamar hukumar Owan West dake jihar Edo a ranar Asabar da yamma.

An kashe jami’an yan sandan ne a mararrabar Uzebba-Aviosi dake hanyar Ifon, Sabongida-Ora. Koda dai babu wani abu da yayi kama da musayar wuta, makisan sun dauke bindigogin jami’an yan sandan da aka kashe.

Wani mazaunin yankin ya ce: “Babu wanda zai iya bayanin abun da ya faru saboda babu karar harbin bindiga, mun dai ga motar yan sanda na ci da wuta, da muka matsa kusa sai muka ga yan sanda hudu na konewa.

An kashe yan sanda 4 sannan aka kona su kurmus a motar sintiri a Edo

An kashe yan sanda 4 sannan aka kona su kurmus a motar sintiri a Edo

“Mutanen da suka aiwatar da wannan aika-aikan sun shirya sosai saboda sun gudanar da aikin ne cikin nasara. Ta yaya mutun zai yi bayanin kisan jami’an yan sanda sannan a zuba gawarwakinsu a cikin motarsu a kuma cinna masu wuta.

“Wannan cibiyar bincike na jami’an ya dade sannan kuma bamu taba ganin wani abu makamancin hakan ba koda kuwa musayar wuta ne a yankin."

KU KARANTA KUMA: 2019: Nasarar APC a Ekiti zai maimata kansa a kudu maso gabas – Magoya bayan Buhari

Da aka kira shi kan lamarin, kwamishinan yan sandan jihar, Mista Babatunde Kokumo, yace ba zai iya Magana kan lamarin ba domin yana jihar Ekiti kan lamarin zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel