Iftila’in gobara ya kone shaguna a wata babbar Kasuwa a Kano
- Tashin wuta a kasuwanni na cigaba da zama sillar gurgunta 'yan kasuwa
- Ko a daren juma'a ma dai gobarar ta lamishe dukiyoyi masu tarin yawa a kasuwar Kofar Wambai dake Kano
Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Kano Alh Sagir Madaki ya bayyana cewa a kalla shaguna guda shida ne su ka kone a kasuwar yari da ke kofar Wambai, sakamakon gobarar da ta tashi a daren ranar Juma'a
Shugaban ya shaida hakan ne lokacin da ya ke ganawa da kamfanin dillanci labarai na kasa (NAN) akan yadda al'amarin ya afku.
"Da Misalin karfe 8:57 na dare na samu kira daga ofishin yan sanda da ke kofar Wambai, in da suka tabbatar cewa an samu tashin gobara a kasuwar yari da ke kofar Wambai.
Jim kadan da samun wannan labari ne na umarci ma'aikatan hukumar tare da daukar motar kashe gobara, inda su ka isa gurin da misalin karfe 9:05 na dare" in ji Sagir Madaki.
KU KARANTA: Tsautsayi: Giwa ta kashe mutane biyu a dajin shakatawa na Yankari dake Bauchi
Ya kara da cewa jami'an hukumar sun dauki kasa da sa'a guda wajen dakile bazuwar gobarar zuwa wasu shagunan, kuma ya ce kawo yanzu suna tsaka da bincike akan musababin faruwar lamarin.
A karshe ya shawarci 'yan kasuwar da sauran al'ummar da ke zaune a yankin, da su kaucewa amfani da duk wani abu da zai haifar da tashin gobara.
Sannan ya shawartar ‘yan kasuwar da su samar da isassun kayan kashe gobara, domin riga-kafin faruwar hakan a nan gaba
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng