Dawo-dawo: Fayemi ya kama hanyar zama sabon Gwamnan Jihar Ekiti

Dawo-dawo: Fayemi ya kama hanyar zama sabon Gwamnan Jihar Ekiti

- Sakamakon zabe sun nuna cewa Fayemi ya kama hanyar nasara

- Yanzu Jam’iyyar APC ce ke kan gaba a zaben Gwamnan Ekiti

- Dr. Fayemi na APC ya fi ‘Dan takarar PDP samun kuri’u a zaben

Mun samu labari cewa idan abubuwa su ka cigaba da tafiya a haka, Jam’iyyar APC ce za ta lashe zaben Gwamna a Jihar Ekiti. Yanzu dai Fayemi ya kama hanyar zama sabon Gwamnan Jihar Ekiti.

Dawo-dawo: Fayemi ya kama hanyar zama sabon Gwamnan Jihar Ekiti

Tsohon Gwamna Fayemi na APC yana daf da lashe zaben Ekiti

Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti kuma ‘Dan takarar APC Dr. Kayode Fayemi na kan gaba kamar yadda Hukumar zabe na kasa ta sanar. INEC ta tabbatar da cewa Fayemi yayi nasara a Kananan Hukumomi 7 da aka fitar da sakamako.

A zaben da ya gudana jiya Fayemi yayi nasara a Karamar Hukumar Ilejemeje da kuri’a 4153 inda PDP ta ke da 3937. A Karamar Hukumar Moba kuwa Kayode Fayemi ya samu 11837, Jam’iyyar PDP ta kuwa ta tashi ne da kuri’u 8520.

A Irepodun-Ifelodun APC ta lashe kuri’u 13,869 inda ‘Dan takarar Fayose ya samu 11,456. A Garin Oye ma dai Mataimakin Gwamna Fayose ya sha kasa inda ya samu kuri’a 11,271, APC kuma ta na da 14,995 inji Hukumar zabe na INEC.

KU KARANTA: An jibga Jami'an tsaro wajen zaben Jihar Ekiti

Shi kuma ‘Dan takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar PDP Farfesa Olusola Eleka yayi nasara ne a Karamar Hukuma daya kacal a Jihar watau a Efon Alaye. Ko a nan dai banbancin da aka samu bai wuce na kuri’a 100 ba kacal.

Olusola Eleka ya fara kokawa da cewa Jami’an tsaro sun hada baki da APC su na murde zaben. Kwanaki kun ji cewa wani babban 'Dan Majalisa Tarayya na Jam’iyyar APC yace zai so ya ga PDP ce tayi nasara a zaben Gwamnan Ekitin.

A Garin Ido-Osi APC ce ma tayi nasara, haka kuma PDP ta sha kasa a Karamar Hukumar Ijero da Gbonyin. Dr. Fayemi yana da kuri’a 87,914 inda ‘Dan takarar PDP ya ke baya da kuri’a 70, 625.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel