Manomi da ya harbi kawunsa ya sami zaman haya a sijin

Manomi da ya harbi kawunsa ya sami zaman haya a sijin

Yan sanda sun kama wani manomi mai shekaru 40, Alex Asante, da ya harbe kawunsa, Kwame Opuku, saboda yana tsamanin dabbar farauta ce ya harba.

Kotu taki amincewa da uzurin da Asante ya gabatar yayin da ya gurfana a gaban alkali Eric Baah Boateng na kotun majistare dake yankin Enchi kamar yadda Adomonline ta wallafa.

Kotu ta umurci shi ya sake bayyana a gabanta a ranar Juma'a 20 ga watan Yuli.

Manomi da ya harbi kawunsa ya sami zaman haya a sijin
Manomi da ya harbi kawunsa ya sami zaman haya a sijin

Dan sanda mai gabatar da kara, ASP Ebenezer Anim Ofori ya ce wanda ya shigar da karar, Kofi Ofosu mamba ne na kungiyar Yan banga na Neigbourhood watch Dog dake kusa da Adjuom a iyakar Enchi.

DUBA WANNAN: An shiga cacar baki tsakanin APC da PDP a kan zargin tura N18bn zuwa Ekiti

Ofori yace a ranar 6 ga watan Yuli misalin karfe 3.30 na yamma wanda ake zargin ya tafi duba tarkon da ya dana a dajin Domoeabra dake kusa da Number Two.

A hanayarsa ta dawowa ne sai ya biya ta gonar kawunsa dake da iyaka da ginarsa don ya dauki wasu kayansa da ya ajiye.

Bayan ya isa gonar sai ya kura wani abu na motsi cikin daji kuma sai ya yi tsamanin dabar farauta ce.

Bayan ya yi harbi, sai ya gane cewa kawunsa ne ke girbe doyansa.

Daga nan ne Asante ya dauki kawunsa zuwa asibitin Samreboi inda aka kwantar dashi daga baya kuma aka tura shi asibitin koyarwa na Komfo Anokye domin a kara duba shi.

Asante ya tafi ya kai kansa kara wajen shugabanin yan banfar Neighbourhood Watchdog inda suka raka shi zuwa ofishin yan sanda dake Enchi inda ya zayyana musu abinda ya faru.

An bar shi ya tafi gida amma daga bisani aka sake kama shi saboda ya taimaka musu wajen bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel