rAPC: 'Dan Majalisar APC Nasiru Garo na nema PDP ta lashe zaben Jihar Ekiti

rAPC: 'Dan Majalisar APC Nasiru Garo na nema PDP ta lashe zaben Jihar Ekiti

Mun samu labari cewa wani babban 'Dan Majalisa Tarayya da ke karkashin Jam’iyyar APC mai mulki yana neman ganin Jam’iyyar PDP ta lashe zaben Gwamna da za ayi a Jihar Ekiti kwanan nan.

rAPC: 'Dan Majalisar APC Nasiru Garo na nema PDP ta lashe zaben Jihar Ekiti

'Dan Majalisar Kano Honarabul Nasiru Sule Garo yana tare da PDP a zaben Ekiti

Honarabul Nasiru Sule Garo wanda ya dade yana wakiltar Gwarzo da Kabo a Majalisar Wakilai ta Tarayya yace zai so ya ga Jam’iyyar PDP tayi nasara a zaben da za ayi na Gwamnan Jihar Ekiti a karshen makon nan.

‘Dan Majalisar wanda yake tare da tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso yana kuma cikin ‘Yan aware na APC da ke karkashin rAPC ya fadi wannan. Babban ‘Dan Majalisar yace bai ji dadin abin da Jami’an tsaro su ka yi a Ekiti ba.

KU KARANTA: Wasu Matasa sun yi tir da danyen aikin Fayose

Sai dai duk da ‘Dan Majalisar na Jihar Kano yayi tir da abin da ‘Yan Sanda su ka yi a Jihar Ekiti daf da zaben nan, Hon. Garo yace Jam’iyyar PDP ba ta da bakin da za ta fito tana kokawa kan abin da aka yi wa Ayo Fayose.

Garo ‘Dan a mutun tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso ne wanda kuma yana cikin mai ba sa shawara a 2003. A 2007 ne Sule Garo ya tafi Majalisar Tarayya. Kwanaki ma dai Sanata Rabiu Kwankwaso ya gana da Fayose.

Kwanaki kun ji labari cewa daya daga cikin Ministocin Shugaban kasa Muhammadu Buhari watau Chris Ngige yayi subul-da-baka ya nemi Jama’an Ekiti su zabi ‘Dan takarar Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa da za ayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel