Yadda wani Saurayi ya kashe Budurwar da ake sa rai zai aura saboda neman Duniya
Mun samu labari daga Jaridar Vanguard kwanaki cewa Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo watau Alhaji Lasisi Oluboyo ya bayyana yadda aka bi aka ga bayan wata ‘Diyar cikin sa mai suna Khadijat kwanan nan.
Lasisi Oluboyo yace ya rasa ‘Diyar sa ne bayan da wanda ake sa ran za ta aura ya dauke ta zuwa ‘dakin sa inda ya shake ta ya kashe ta har lahira. Oluboyo yace wanda ake zargin ya birne gawar yarinyar ne a karkashin gadon sa saboda lakani na wani tsafi da aka ba sa.
Mahaifin wannan Marigayiya wanda ya taba rike mukamin Mataimakin Gwamna a Ondo, ya bayyana cewa zai so ya fawwalawa Ubangiji komai sai dai kuma gudun hakan ta kara faruwa. Wannan abu dai ya faru ne a Oke Aro da ke cikin Garin Akure da ke Jihar ta Ondo.
KU KARANTA: Da dukiyar barayi Buhari ya ci zabe - PDP
Wannan yarinya tayi mako kusan guda ba a gan ta ba bayan da wannan yaro ya dauke ta daga Makaranta Inji Mahaifin ta. Har sai da ta kai kawayen ta sun soma neman ta a makaranta yayin da aka dauka cewa ta tafi gida ne bayan an kammala darasin makon.
A baya kun ji cewa an ga gawar Marigayiya Khadjijat Adenike Oluboyo ne a karkashin gadon saurayin na ta wanda aka fi sani da Q.S. Ashe ma dai saurayin ya haka rami ne ya birne ta bayan yayi amfani da ita wajen wani tsafi na sa ini Mahaifin ta Lasisi Oluboyo.
Dazu kun ji labari mai ban takaici na cewa an kashe wani mutumi har lahira saboda banbancin siyasa kurum da ya samu da wasu Bayin Allah a wajen taro. Wannan abu mara dadi ya faru ne a Kofar Doka a cikin Garin Zaria da ke Kaduna cikin 'yan kwanakin nan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng