Rikicin siyasa yayi sanadiyyar mutuwar wani ‘Dan APC har lahira a Zaria

Rikicin siyasa yayi sanadiyyar mutuwar wani ‘Dan APC har lahira a Zaria

- Yanzu dai harkar tsaro na kara jagwalgwalewa a cikin kasar nan

- Daga samun sabanin siyasa aka kashe wani mutumi a Garin Zaria

- An kashe wani ‘Dan APC ne saboda kurum sun yi wata ‘yar rigima

Mun samu labari mai ban takaici na cewa an kashe wani mutumi har lahira saboda siyasa kurum da ya samu da wasu Bayin Allah. Wannan abu mara dadi ya faru ne a cikin Garin Zaria da ke Kaduna.

Wani Bawan Allah da abin ya faru kusa da shi ya bayyana mana cewa kwanan nan aka kashe wani mutumi bayan ya sabu sabani da Abokan siyasan sa. Jim kadan da sabun wannan sabani inda aka yi ta gardama ne aka kashe shi.

KU KARANTA: Kalaman da Buhari yayi a shekarun baya sun dawo su na cin sa

Wasu ne wanda har yau ba a san su ba su ka kashe wannan mutumi ana zaune kalau. Bayan sun hallaka wannan sanannen ‘Dan siyasa ne sai su ka jefa gawan sa a ofishin Jam’iyyar APC da ke kusa da kofar Doka a kan hanyar Jos.

Ko da har yanzu sunan wannan Bawan Allah bai bayyana mana ba, wannan abu ya faru ne a cikin Garin Zaria da ke cikin Jihar Kaduna a Arewacin Najeriya. Marigayin yayi ‘yar gardama ne da wasu ‘Yan APC ana gobe za a kashe shi.

Jiya kuma kun ji cewa aiki a Gwamnatin APC na nema ya zama kayan gabas inda sai su wane-da-wane su ke iya samu. ‘Yan Majalisu da manyan mukarabban Gwamnati na Fadar Shugaban kasa da Sarakuna ne ke yin yadda su ka so.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags:
APC