An janye Yansanda daga gidan gwamnan Ekiti Fayose bayan korafin jama'a
- Ance duk tsoron kar jiharsa ta koma hannun APC ne yake ta rara-gefe
- Yansanda sun yiwa gidan gwamnatin kawanya, amma yanzu sun janye
- A baya Fayose yayi rashin kunya wai shugaban kasa bai isa yaje jiharsa ba
An janye yan sandan kofofin shiga gidan gwamnatin jihar Ekiti da ofishin kamfen na Kolapo Olusola dake titin Fajuyi, dake Ado Ekiti.
Zanga zangar da yan sanda sukayi a ranar talata, wanda suka yi a kofar lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yaje babban rally na jam'iyyar APC a ranar laraba. Shugaban ya hanzarta barin jihar bayan angama rally din.
DUBA WANNAN: An gano alakar jarabar son mata da tabin hankali
Sun tarwatsa yan jam'iyyar PDP da magoya bayan su daga ofishin a ranar laraba cewa ana taron ne ba da izini ba.
Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa, kofofin gidan gwamnatin a bude suke babu tsaron shige da ficen ababen hawa a ranar Alhamis.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng