Kwarankwatsa ta hallaka dan acaba da wasu mutane biyu a Ogun

Kwarankwatsa ta hallaka dan acaba da wasu mutane biyu a Ogun

Mutane uku ciki har da dan acahaba sun rasu sanadiyar fadowar da kwarankwatsa tayi akansu a Ijebu-Ode ta jihar Ogun. Lamarin ya faru ne a yau Alhamis bayan anyi wani ruwa kamar da bakin kwarya a garin.

Mutanen da suka rasu dai matasa ne masu shekaru kasa da 30 kuma suna hanyar su ta neman wajen fakewa a ginin wani Otel mai suna Gateway dake kusa da gidan gwamnan jihar ne kwarankwatsar ya fado musu kuma ya halaka su duka.

DUBA WANNAN: Sai an kori bara-gulbi daga cikin jami'an soji sannan za a iya shawo kan kashe-kashe a Najeriya

An gano cewa su hudu ke tafiya yayin da kwarankwatsar ta fado musu amma mutum na hudun ya yi sa'a abin bai shafe shi ba kuma daga baya ya har wajen cikin hanzari.

Kwarankwatsa ta hallaka dan acaba da wasu mutane biyu a Ogun

Kwarankwatsa ta hallaka dan acaba da wasu mutane biyu a Ogun

Wani wanda yazo wuce a hanya mai suna Ridwan, yace ya gane daya daga cikin wanda suka mutu inda yace sunansa Ayo kuma dan asalin kauyen Imomo-Ijebu ne dake karamara hukumar Ijebu ta Arewa a jihar.

Yace Ayo yana gyran fanka kuma yana sana'ar achaba.

The Nation ta gano cewa mutane da dama sun taro suna kallon gawawakin amma babu wanda ya dauke su daga hanya soboda suna tsoron abinda ka iya biyo baya idan suka taba gawar da kwarankwatsa ya kashe kamar yadda mutanen garin suka camfa.

Har jami'an Hukumar 'yan sandan Najeriya da suka ziyarci wajen sun ki dauke gawawakin daga titin kuma sun ki taba jakunkunan matasan balle a gano mene ke cikin jakunkunan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel