Tsautsayi: Giwa ta kashe mutane biyu a dajin shakatawa na Yankari dake Bauchi

Tsautsayi: Giwa ta kashe mutane biyu a dajin shakatawa na Yankari dake Bauchi

- sha'awar kallon giwaye ta zama sanadiyyar rasa rayukan wasu mutane biyu

- Ana zargin giwayen sun kashe mutanen ne sakamakon firgita da suka yi yayin da ake daukar su a hoto

- Jama'a sun taru suna daukan hotunan giwayen bayan sun kubuce daga inda ake tsare da su

Hukumar kula da dajin shakatawa da yawon bude idanu na Yankari dake jihar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar mutane biyu sakamakon karon batta da giwaye a kauyen Bajama dake daf da gandun dajin na Yankari.

Bayanin yadda lamarin ya afku na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban gudanar da dajin, Habu Mamman, ya biawa manema labarai a jihar Bauchi, a jiya Alhamis, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar 8 ga watan Yuli, bayan giwayen sun fice daga inda aka taskancesu kuma suka bazama zuwa kauyen na Bajama da sassafe.

Tsautsayi: Giwa ta kashe mutane biyu a wurin shakatawa na Yankari dake Bauchi
Tsautsayi: Giwa ta kashe mutane biyu a wurin shakatawa na Yankari dake Bauchi

Jawabin ya kara da cewa, “Giwayen sun isa har dajin Gwartanbali inda mazauna kauyukan kewayensa suka fito suka kewaye su suna ta daukar hoto tare da su”.

“Ifila’in ya afku ne bayan da Giwayen suka fusata suka tarwatsa dandazon mutanen, inda garin gudun tsiran ne jama’a suka ture wani yaro mai suna Fa’izu Chiroma Musa dan shekara 8, wanda hakan ta sa daya daga cikin Giwayen ta take shi”. Hakan ta faru ne da misalin karfe 10:00 na safe.

Sanarwar ta kara da cewar, mutanen kauyen sun rinka bin Giwayen suna daukar hoto tare da su har sai da garin daukar hoton wata Giwar ta buge wani mai suna Malam Haruna Abubakar, wanda nan take ya fadi matacce da misalin karfe 4:00pm na yamma.

”Kwararrun ma’aikatanmu dake kula da namun dajin sun shafe awanni suna kokarin dawo da Giwayen inda ake tsare su sakamakon yawaitar mutanen da suke ta binsu.

KU KARANTA: Makiyayi ya kashe wani sufeton dan sanda a Kebbi

"Akasari idan irin haka ta faru ma’aikatanmu su kan kai dauki cikin gaggawa don dawo da dabbobin inda ake tsare da su, amma a wannan karon abin ya ba su wahala saboda cincirindon mutanen da suke ta son taba su ko daukar hotonsu." Habu Mamman ya bayyana.

Shugaban masu kula da gandun ya tabbatar da cewa samun aran-gama tsakanin Giwaye da mutane ba abu ne sabo ba a gandun dajin, amma dai an dade ba’a samu asarar rai ba.

Daga karshe ya ce “Mun ziyarci iyalan wadanda abin ya shafa kuma sun shaida mana cewa laifinsu ne da suka matsa kusa da Giwayen sosai don ba su san suna da hadari haka ba”.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng