Mace-mai-kamar-maza: Labarin wata mata mai sana'ar Keke Napep a Najeriya

Mace-mai-kamar-maza: Labarin wata mata mai sana'ar Keke Napep a Najeriya

Wata mata mai matukar hazaka da son neman na kanta da kuma aka sakaya sunan ta ta bayar da tarihin rayuwar ta mai cike da ban tausayi inda ta bayyana yadda ta soma sana'ar tukin keke napep bayan rasuwar mijin ta.

Matar dai ta bayyana cewa tana da 'ya'ya uku ne lokacin da mijin ta ya rasu ya barta da tsohon ciki da kuma halin rashi da kuncin rayuwa.

Mace-mai-kamar-maza: Labarin wata mata mai sana'ar Keke Napep a Najeriya

Mace-mai-kamar-maza: Labarin wata mata mai sana'ar Keke Napep a Najeriya

KU KARANTA: Rahama Sadau ta girgiza dandalin zumunta da sabbin hotuna

Legit.ng ta samu cewa sai dai matar ta bayyana a cikin firar da akayi da ita cewa da tana sana'ar saida kayan sanyi ne amma kuma sai wasu marasa imani suka yi mata fashi suka kwace mata dukkan kayan sana'ar ta.

Daga baya matar ta kuma bayyana cewa sai ta fara sana'ar tireda bayan ta nemi bashi daga wurin abokan ta amma ita ma sana'ar tazo ta durkushe.

Ta cigaba da cewa daga nan ne kawai sai ta yanke shawarar ta anshi bashin keke napep din domin ta rika nemawa kanta da 'yayan ta rufin asiri.

Daga karshe ta kuma bayyana cewa tana fatan ta bar sana'ar tata da zarar ta samu wata madadin ta domin tana cike da hatsarin gaske.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel